Litinin 9 Nuwamba 2026 - 08:00
Shawarwarin Tarbiyya na Ayatullah Ha’iri Shirazi Game Da Girmama Yaro

Hauza/ Mu'amalantar yaro a matsayin sarki mai iko ba yana nufin a bar shi ba tare da kulawa bane; ana iya ba wa ɗa umarni, a yi masa gargaɗi, a kuma yi masa nasiha mai kyau, amma ya kamata a yi magana da shi kamar ana magana da wanda ya fi shi girma, tare da mutunta matsayinsa.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ruwayar "الوَلَدُ سَیّدٌ سَبعَ سِنینَ” ba tana nufin a bar yaro ya yi duk abin da yake so ba tare da wani sharadi ba ne. Ayatullah Ha’iri Shirazi, yayin da yake bayyana ma’anar wannan ruwaya, ya jaddada muhimmancin kiyaye mutuncin ɗa yayin ba shi umarni ko kuma yi masa gargaɗi, yana mai cewa a ɗauki yaro a matsayin sarki.

Kasancewar yaro a matsayin babban mutum ko sarki ba yana nufin kada ku gaya wa yaro komai bane. Har zuwa shekara bakwai, A’a! idan kana son ka ba yaro umarni, ka ba shi; amma ya kasance ba kamar umarnin da za ka ba wanda ya fi sa girma bane; ka faɗa masa kamar yadda za ka yi magana da sarki! Ruwayar “الوَلَدُ سَیّدٌ سَبعَ سِنینَ” ba tana nufin a bar yaro haka kawai ba. Ko kaɗan! Kayi masa nasiha; ka yi masa gargaɗi; amma ta hanyar da kake magana da wanda ya fi sa girma. Kada ka ɗauke shi a matsayin yaro ƙarami; ka ɗauke shi a matsayin sarki.

Madogara: Littafin Rah-e Roshd, juzu’i na 2, shafi na 26.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha